Ka bamu Kunya ina fatan Gwamna Ganduje zai ja maka Kunne>>Hadimin shugaban kasa yawa Kwamishinan Kano da yayi murnar Mutuwar Abba Kyari magana
Kwamishina a Kano, Injiniya, Mu’azu Magaji da yayi murnar mutuwar shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Abba Kyari na ci gaba da daukar Hankali.
Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya mayar da martani kan wannan lamari.
Yace abin kunyane abinda Injiniya Mu’azu Magaji yayi kan mutuwar Abba Kyari. Ya kara da cewa
an ga Kwamishinan a bainar jama’a a shafinshi na Facebook yana murnar mutuwar Abba Kyarin. Ya kara da cewa yana fatan Allah gwamnatin Kano da Gwamna Ganduje zasu ja mai kunne.
Bashir ya kara da cewa idan wasu kalilan mutane da suka bace suka yi irin wannan abu da kwamishinan yayi, za’a iya mantawa ko kuma a kauda kai amma abinda kwamishinan yayi a matsayinshi na me fada aji,abin takaicine.